Fada na ci gaba a birnin Mogadishu | Labarai | DW | 31.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fada na ci gaba a birnin Mogadishu

A kasar somalia fada na ci a babban birnin kasar Mogadishu inda sojojin gwamnati dana Habasha suke ci gaba da fafatawa da sojin sa kai.

Wannan shine fada mafi muni tun 1991 wanda ya tilasatawa daruruwan mutane ficewa daga birnin.

A dai jiya jumaa ne aka harbo wasni jirgi mai saukar angulu na Habasha yayinda kuma wani bam ya fada kann wani asibiti inda mutane da dama suka rasa rayukansu.

Gwamnatin kasar Habsaha dai tace sojojinta sun kashe yan bindiga fiye da 200 tun da fadan ya barke.

Kakakin gwamnatin Hussein Muhammad hussein ya dora laifin wannan fada kann wadanda ya kira yan alqaeda.