1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta tallafa wa zaman lafiya a Afganistan

Abdourahamane Hassane
March 28, 2019

Kantomar Kungiyar Tarrayar Turai kan manufofin ketare Frederica Mogherini ta ba da shawara kawo sauye-sauye a fannin tsaro a Afganistan ta hanyar shigar da tsoffin mayakan Taliban a cikin rundunar sojojin kasar.

https://p.dw.com/p/3FqV5
Afghanistan Konferenz in Brüssel Ghani mit Tusk und Mogherini
Hoto: Reuters./F. Lenoir

Har kawo yanzu dai akwai sauran rina a kaba game da sha'anin tsaro a Afganistan. A makon da ya gabata akalla mutane guda 13 suka rasa rayukansu galibi fararan hula wadanda suka hada da mata da yara kanana a wani hari ta jiragen yaki na sama da dakarun rundunar kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa da ke Afganistan suka kai kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana. Daga cikin wadanda suka mutu har da yara guda goma yan gida guda wadanda suka gujewa fadan da ake domin zuwa Kunduz

Taron shugabannin al'umma a Afghanistan
Taron shugabannin al'umma a AfghanistanHoto: DW/S. Tanha

Wannan ya sa dubban jamaa yin gangami a yankin domin yin Allah wadai da Amirka tare da bayyana cewar ba su laminta da hare-haren da mayakan sama na Amirkan ke kaiwa a Afganistan ba. A shekara ta 2018 a cikin wata sanarwa da ta bayana hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya a Afganistan UNAMA ta ce adadin da ake kashewa na farar fula a yakin na dada karuwa. Richard Bennet shine shugaban hukumar ta agajin ta Majalisar Dinkin Duniya a Afganistan

“An kashe farar hula 3804 a shekara ta 2018 a cikinsu akwai yara wadanda yawansu ya kai 1000 maza da mata yayin da gabadaya a yakin aka kashe farar hula dubu 10993 kawo yanzu

Afghanistan, Nangarhar:  Demonstrationen gegen Militäreinsatz
Zanga zangar wasu jama'a a AfghanistanHoto: DW/O. Deedar

Hare-haren bama bamai da kungiyar Taliban ke kaiwa da kuma kungiyar mayakan IS su ne dalilai na mafi yawan mutuwar fararan hular da ake samu a Afganistan ko da shi ke akan kashe fararn hular a lokacin hare haren da dakarun Afganistan da na Amrika ke kaiwa kamar yadda kwamshina hukumar ta UNAMA Bennet ya bayyana.

“Mun damu ainin da yawan karuwar wadanda lamarin ke rutsawa da su a sakamakon hare hare ta jiragen sama na yaki na dakarun kasa da kasa a Afganistan wanda adadin ya kai kusan kashi 60 ciki dari a shekara bara kawai da ta shige”

An dai kwashe kusan tsawon wata guda Amirka na jogarancin wani shirin tattaunawa da ‘yan kungiyar Taliban domin kawo karshen yaki da kuma ficewar rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasa da kasa a Afganistan, sai dai har yanzu abin ya gaggara yayin da a waje guda dakarun Jamus dake a Afganistan din aka kara tswaita waadinsu da shekara guda a kwanan nan.