EU: Za ta taimaka wa ′yan gudun hijira a Girka | Labarai | DW | 27.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU: Za ta taimaka wa 'yan gudun hijira a Girka

Kwamitin zartaswa na Kungiyar Tarrayar Turai ya ba da sanarwa bullo da wani tsari na jin kai na taimaka wa 'yan gudun hijira da ke a kasar Girka.

Sabon tsarin wanda za a kashe kudade har Euro miliyan 209 kamar yadda babban kwamishina kungiyar ya bayyana zai taimaka wajen kyautata halin rayuwar masu neman mafaka. Wadanda ya ce a maimakon sauke su a gidajan bai daya zai ba da damar a rika daukar musu gidajan haya tare da daukar dauwainiyar su ta abinci da magunguna.