1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

EU za ta sake matakai a kan zirga-zirga

January 22, 2021

Shugabbanin kungiyar Tarayyar Turai, sun yi gargadi da kakkausar lafazi game da bukatar al'umar kasashe mambobinta su dakatar da tafiye-tafiyen da ba su wajaba ba.

https://p.dw.com/p/3oGeD
Belgien Brüssel | Pressekonferenz Ursula von der Leyen und Charles Michel
Hoto: Thierry Monasse/AA/picture alliance

Shugabannin da suka gargadin, sun ce sabbin matakan hana zirga-zirga na nan tafe nan ba da jimawa ba muddin aka gaza hango alamun sa'idar annobar corona da ta zo ta wata sigar.

Shugabar hukumar gudanarwar Tarayyar ta Turan, Ursula von der Leyen tare da jagoran majalisar kungiyar, Charles Michel, wadanda suka yi wannan gargadi a ranar Alhamis, suna magana ne ganin yadda wasu kasashen yankin ke sakaci da matakan hana yaduwar cutar.

Duniya dai ta sake shiga wani sabon rudani game da wannan annoba, bayan bullar sabon nau'inta daga Birtaniya wato tsohuwar mamba a kungiyar, inda ya zuwa yanzu annobar ke ci gaba da ta'asa tare da kama mutane cikin hanzari.