1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta matsa wa na hannun damar Shugaba Kabila

December 7, 2018

Tarayyar Turai na shirin daukar mataki kan wanda ke shirin gadon mulkin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Emmanuel Ramazani.

https://p.dw.com/p/39gej
Kongo Emmanuel Ramazani Shadary
Hoto: REUTERS

Kungiyar Tarayyar Turai, ta shirya kakaba takunkumi kan wanda Shugaba Joseph Kabila na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ke ra'ayin ya gaje shi, makonni biyu kafin gudanar da babban zaben kasar.

Jami'in kungiyar ta EU sun ce daga cikin matakan da za a dauka kan dan takaran na jam'iyya mai mulki a Kwango Emmanuel Ramazani, sun hada da haramta masa tafiye-tafiye da kuma rike masa kadarori, da za a sabonta.

Takunkumin za kuma su shafi wasu karin mutum 15, da ake sa ran ministocin harkokin wajen kasashen Turan za su amince ba tare da wata doguwar muhawara ba, lokacin wani zama a ranar Litinin da ke tafe.

A bara ne aka zargi dan takaran na Kwango Mr. Ramazani, da yi wa zaben Kwangon katsa-landa da ma afka wa masu zanga-zangar adawa da jinkirin zabe a kasar.