EU za ta daidaita hulda da Turkiyya | Labarai | DW | 05.04.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU za ta daidaita hulda da Turkiyya

Bayan shafe dogon lokaci suna zaman doya da manja, Kungiyar Tarayyar Turai za ta gabatar wa Turkiyya da sabon jadawalin dawo da huldarsu a ranar Talata mai zuwa.

Shugabar hukumar gudanarwa ta kungiyar EU Ursula von der Leyen da na majalisar Turai Charles Michel, za su yi wata ganawa da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a birnin Ankara, domin kara tantance batutuwan da suka shafi huldar bangarorin biyu ciki har da batun tattalin arziki da na 'yan gudun hijira da ke jibge a Turkiyya, kamar yadda taron kolin shuwagabannin kungiyar na ranar 26 ga watan Maris ya gindaya.

Sai dai wannan lamarin na zuwa ne, bayan da kungiyar ta ce ta lura da Shugaba Erdogan ya sassauto daga matsayarsa ta zaman wani shu'umi kan batutuwan da suka shafi kasar Turkiyya da nahiyar Turai.