1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin EU za su ci gaba da zama a gabar tekun Libiya

Binta Aliyu Zurmi
March 17, 2021

Hukumar tarayar Turai za ta kara wa'adin ayyukan dakarun sojinta a tekun Bahar Rum da shekaru biyu domin ci gaba da saka idanu a haramcin safarar makamai a kasar Libiya.

https://p.dw.com/p/3qmJk
Konflikt Türkei | Frachtschiff | Kontrolle durch deutsche Soldaten
Hoto: Demiroren News Agency/AFP

Kungiyar ta EU ta fidda wannan sanarwar ne a wannan rana ta Laraba, ta bakin wani babban jami'inta.

Jami'in ya ce a mako mai zuwa ne za a kai karshen wannan batu, wanda zai ba da damar ci gaba da girke dakarunsu har nan da karshen watan Maris din shekarar 2023.

Tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Mu'ammar Ghaddafi makamai suka fara bazuwa daga kasar zuwa wasu kasashen Afirka da yanzu suke fama da matsalolin tsaro.

A baya babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres ya yi kira ga kasashen duniya da su yi hobbas wajen kawo karshen rikicin kasar ta Libiya ko a sami dakile bazuwar da makamai ke yi a ko ina.