1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta kasa sasanta rikicin Balkan

Ramatu Garba Baba
August 18, 2022

Tarayyar Turai ta sanar da ci gaba da kokarinta na sasanta rikicin Kosovo da Sabiya bayan da aka tashi daga zaman sulhun ba tare da an cimma matsaya ba.

https://p.dw.com/p/4FkXz
NATO Serbien Kosovo Gespräche
Hoto: Olivier Matthys/dpa/picture alliance

An tashi daga taron sasanta Sabiya da Kosovo na wannan Alhamis, ba tare da an cimma matsaya ba. Tarayyar Turai wacce ta kira taron da zummar shiga tsakanin don samar da daidaito a tsakanin makwabtan a birnin Brussels na kasar Beljiyam, ta ce, hakan ba zai sa ta yi kasa a gwiwa ba, saboda haka za a ci gaba da tattaunawar nan gaba.

Sabani a tsakanin yankunan biyu, ya samo asali ne daga takaddama kan mallakar lasisin mota kafin shiga kasar juna, wanda daga bisani ya rikide zuwa tarzoma. A shekarar 1999 Kosovo ta balle daga Sabiya, kafin ta aiyana kanta a matsayin kasa mai cin gashin kanta a shekarar 2008.