Kosovo wata karamar kasa ce da ke jerin kasashen da ke yankin Balkans. Kasar na da mutane da yawansu ya kai miliyan daya da dubu dari takwas.
A cikin shekara ta 2008 ne kasar Kosovo da ke da yawan Musulmi ta samu 'yancin kanta daga Serbiya. Ko da dai an yi yunkurin neman 'yancin kan tun a shekarun 1990 amma hakan bai samu ba, sai ma rikici da kasar ta tsunduma ciki wanda ya sanya dakarun tsaro na NATO suka shiga don daidaita al'amura a shekarar 1999.