1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Turai ta kakkabawa Rasha sabbin takunkumai

Ramatu Garba Baba
February 22, 2021

Kungiyar tarayyar Turai ta yanke shawarar kara kakkabawa Rasha takunkumi a sakamakon hukuncin dauri da kotu ta aiwatar kan madugun adawar kasar Alexie Navalny.

https://p.dw.com/p/3pj08
Russland | Moskau | Russischer Oppositionspolitiker Alexej Nawalny vor Gericht
Hoto: Vladimir Gerdo/TASS/dpa/picture alliance

Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas, ya fada wa manema labarai jim kadan bayan kammala taron da suka yi a birnin Brussels cewa, ba su da zabi face daukar matakin sanya takunkumin. Sa-in-sa tsakanin bangarorin biyu dai, ya biyo bayan kama jagoran adawa Alexei Navalny kuma mai caccakar gwamnatin Shugaba Vladimir Putin, bayan da ya dawo daga jinyar da ya yi a Jamus a sanadiyar gubar da aka sanya masa. 

Kungiyar EU mai mambobin kasashe 27, ta kuma sanya takunkumi ga wadanda ke da hannu a sanya wa madugun adawar guba, sai dai Lauyan Navalny ya bukaci a sanya musu takunkumin tafiye - tafiye da toshe asusun ajiyar manya 'yan siyasa da ke zama na hannun daman Shugaba Vladimir Putin. Kotu a kasar ta yanke wa Navalny hukuncin zaman gidan yari na shekaru uku da rabi.