1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta aminta da sakamakon zaben Pakistan

Yusuf Bala Nayaya
July 27, 2018

Jagoran masu sanya idanu daga Kungiyar EU Michael Gahler ya bayyana zabe da cewa ya yi kyau amma tsarin da aka bi kafin zabe da gyara a ciki.

https://p.dw.com/p/32Dbf
Wahl in Pakistan
Hoto: Getty Images/A.Ali

Masu sanya idanu daga Kungiyar Tarayyar Turai sun amince da yadda zabe ya gudana a kasar Pakistan, sai dai sun bayyana rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da yakin neman zabe, ga yadda aka rika yi wa kafafan yada labarai barazana, da ma barazana ga 'ya'yan tsohuwar jam'iyya mai mulki. Masu sa idanu daga EU 120 ne, sun kuma ziyarci wuraren kada kuri'a 582, da mazabu 113.

Jagoran masu sanya idanu daga Kungiyar EU Michael Gahler ya bayyana wa manema labarai a birnin Islamabad cewa yadda aka yi tsare-tsare da yakin neman zabe a 2013 ya fi kyau idan aka kwatanta da yadda aka yi a wannan shekara ta 2018.