EU: Matsalar kwararar bakin haure na kara kamari | Duka rahotanni | DW | 18.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Duka rahotanni

EU: Matsalar kwararar bakin haure na kara kamari

Kungiyar Tarrayar Turai ta tattauna kan batun dakile kwararar bakin haure daga Libiya zuwa Italiya a wani mataki na rage asarar rayukan jama'a da ke faruwa a kogin Baharum.

Ministocin harkokin waje na kasashen Kungiyar Tarrayar Turai sun gudanar da wani taro a birnin Brussels na kasar Beljiyam wanda ya tattauna batun kokarin dakile kwararar bakin haure daga Libiya zuwa Italiya ta jiragen ruwa marasa inganci. Taron ya nuna cewar duk da irin matakan da ake dauka na rage asara rayukan jama'a da kuma yaki da kwarararan bakin hauren, babu wani ci gaba da aka samu sai ma koma baya. Kungiyar Tarrayar Turan na da wasu manyan rundunoni guda biyu da ta ce an girke tun a shekara ta 2015 da suka hada da rundunar sojin ruwa ta Triton wacce aikinta shi ne na ceto 'yan ci ranin da suka tagayyara a gabar tekun Siciliya da Lampedusa na Italiya, sai kuma Sophia wacce aikinta shi ne na taro masu dauko fasinjar 'yan cirani cikin jiragen ruwa na roba wadanda ke tasowa daga Libiya. Sai dai duk da haka bayyanai na nuna cewar duk da irin yunkurin da aka sha yi na ceto yan cirani da suka galabaita adadadin wadanda ke mutuwa a ruwan teku  shi ma yana karuwa.

A  farkon watannin shida na wannan shekarar 2017 sama da mutane dubu biyu suka mutu a gabar ruwan na Italiya, kana kuma duk da aikin da rundunar Sophia ta ke yi na kama masu yin safarar 'yan ciranin, an gano cewar su ma adadinsu na karuwa, yayin da tun daga farkon wannan shekara zuwa yanzu bakin haure kusan dubu 86 galibi 'yan kasashen Afrika suka isa a gabar tekun Italiya. Wannan kuma na daya daga cikin dalilian da ya sa ministocin kasashen kungiyar Tarrayar Turai suka ki amincewa da tsawaita wa'adin rundunar sojin ruwa ta Sophia da ke aikin farautar masu safarar 'yan cirani wanda wa'adinta ke cikawa a karshen wannan watan na Yuli.

Barazanar Italiya ta bai wa 'yan cirani izinin shiga Turai

Gwamnatin kasar Italiya wacce ita ce ke karbar dubban 'yan ci rani ta yi barazanar barin bakin tare da bai wa 'yan cirani akalla dubu 200 visa domin su fantsama a cikin sauran kasashen Turan idan har kasashen ba su ba ta tallafi ba kamar yadda aka tsara tun farko.Italiya ta nuna damuwarta a game da yadda kungiyoyi masu zaman kan su da dama ke da jiragen ruwa wadanda ke yin aikin ceton 'yan cirani wanda suke ganin hakan na taimakwa wajen kara samun masu yin safarar 'yan ciranin ta barauniya hanya zargin da daya daga cikin kungiyar SOS Meditranien ta musunta. A na shi bangaren Ministan harkokin waje na kasar Austriya Sebastian Kurz ya ce abin da ya kamata a yi shi ne na tare hanyar da 'yan ciranin ke bi ta tekun Bahrum. Daga  karshe  taron na Kungiyar Tarrayar Turai ya yanke shawarar haramta sayar da jiragen ruwa na roba da injinan jiragen da ake sayarwa Libiya domin yaki da kwararar bakin hauren ganin  masu safarar 'yan ciranin na yin amfani da irin jiragen.

Sauti da bidiyo akan labarin