Erdogan ya bayyana Assad da dan ta′adda | Labarai | DW | 27.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Erdogan ya bayyana Assad da dan ta'adda

Shugaban Turkiyya Racep Tayyip Erdogan ya bayyana shugaba Bashar al Assad na Siriya a matsayin dan ta'adda.

Shugaban Turkiya Racep Tayyip Erdowan da takwaransa na Tunusiya Beji Caid Essebsi

Shugaban Turkiya Racep Tayyip Erdowan da takwaransa na Tunusiya Beji Caid Essebsi

Erdogan ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da suka gudanar kai tsaye da takwaransa na Tunusiya Beji Caid Essebsi a gidan talabijin, a wata ziyarar aiki da yake yi a yanzu haka a Tunusiyan. Erdogan ya ce tabbas Assad dan ta'adda ne, kuma abu ne mai matukar wahala ya ci gaba da kokarin sulhunta rikicin Siriyan da shi, yana mai cewa ta ya za su yi aiki domin samo mafita ga Siriya da mutumin da ya kashe miliyoyin al'ummarsa? Tun da fari dai Erdogan ya kai ziyara kasashen Sudan da Chadi inda ya sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro da tattalin arziki da kasashen biyu.