Ecowas na tattauna batun rufe iyakokin Najeriya | Labarai | DW | 16.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ecowas na tattauna batun rufe iyakokin Najeriya

Wakilan kasashen yankin yammacin Afirka na kungiyar Ecowas sun soma wani taro  a birnin Ougadougou na Burkina Faso, domin samar da hanyoyin na mafita a game da matakin da Najeriya ta dauka na rufe iyakokinta.

Taron wanda ya hada ministocin  harkokin waje da na kasuwanci na kungiyar  Ecowas, ya yi tsokaci a game da matakin na rufe iyakokin da Najeriya ta yi wadanda suka ce ya sabama yarjejeniyar kasuwanci da ke a tsakanin kasashen. A cikin watan Augusta ne  gwamnatin Najeriya ta rufe iyakokinta saboda dalilan da ta kira na dakatar da fasa kobri na shigo da shinkafa da kuma kaji da ta ce  ake shigomata da su daga Jamhuriyar Benin.