Ebola ta kama jami′in Majalisar Dinkin Duniya | Labarai | DW | 24.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ebola ta kama jami'in Majalisar Dinkin Duniya

Mutum na hudu cikin ma'aikata da ke aiki karkashin shirin ayyukan Majalisar Dinkin Duniya a Laberiya, kasar da annobar Ebola ta addaba ya kamu da cutar bayan wani gwaji.

Wannan dai shi ne karo na hudu da aka sami wani jamai'i cikin rundinar wanzar da zaman lafiya a Laberiya ta UNIMIL, da ya kamu da wannan cuta a daidai lokacin da dakarun ke jimamin mutuwar 'yan uwansu biyu da suka rasu ta sanadin wannan cuta watanni uku da suka gabata, kamar yadda sanarwar da jami'an na Majalisar Dinkin Duniyar da ke aiki a kasar ta Laberiya suka nunar a yau Laraba.

Laberiya dai ta kasance kasa da ke kan gaba wajen yawan wadanda suka rasu ta sanadin cutar Ebola a duniya inda aka samu mutane 3,376 da suka rasa ransu saboda wannan annoba. Sai dai a wata guda da ya gabata ana ganin raguwar wadanda ke rasuwa ta sanadin wannan cuta a kasar.

Sama da mutane 7,500 suka rasu ta sanadin cutar Ebola a yammacin na Afrika.