Ebola: Najeriya ta bada tallafin likitoci | Labarai | DW | 03.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ebola: Najeriya ta bada tallafin likitoci

Rahotanni daga Najeriya na cewar akalla jami'an kiwon lafiyar kasar 250 aka aike don bada tallafi wajen kawar da cutar Ebola a wuraren da ta yi kamari.

Wannan adadi na ma'aikatan lafiyar da Najeriya ta bada na daga cikin kimanin 1000 da kungiyar kasashen Afirka ta AU ta ce za ta tura kasashen Liberiya da Gini da kuma Saliyo don agazwa wandanda ke can da nufin kawar da annobar.

Gabannin tafiyar ma'aikatan na Najeriya dai, kasashen da ke fama da cutar sun yi korafi dangane da jan kafar da suka ce an kafin fara tura wanda za su taimaka musu.

Cutar Ebola dai ta yi sanadin rasuwar kimanin mutum sama da dubu 6 daga cikin dubu 17 da aka bayyana cewar sun kamu, yayin da ake cigaba da fafutuka wajen samo maganin rigakafin cutar.