Ebola: Amirka ta ce akwai jan aiki | Labarai | DW | 18.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ebola: Amirka ta ce akwai jan aiki

Shugaban Amirka Barack Obama ya ce har yanzu akwai jan aiki a gaban kasashen yammacin Afirka dangane da yakin da ake yi da cutar nan ta Ebola.

Obama ya ce akwai buƙatar ƙara matsa kaimi wajen yaƙar cutar wadda ya ce barazana ce ga duniya baki daya muddin dai ana ci gaba da samun bayyanarta da ma yaɗuwarta tsakanin mutane.

A wata zantawa da ya yi a fadar White House da jami'an da ke jagorantar yaƙi da cutar a ƙasar, shugaban ya nemi da lallai su kara matsa lamba wajen ganin an kiyaye ƙasar daga barazanar wannan cuta.

Obama har wa yau ya buƙaci 'yan majalisar dokokin Amirka kafin tafiyarsu hutun ƙarshen shekara da su amincewa buƙatar da ya miƙa musu ta yin amfani da dalar Amirka miliyan dubu shidda da kusan rabi don daƙile bazuwar cutar tun daga tushe.