Dubban rayuka sun salwanta a Syria | Labarai | DW | 13.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dubban rayuka sun salwanta a Syria

Wani bincike ya bayyana cewa yakin kasar Syria ya cinye rayukan mutane sama da dubu 350, yayin da rabin yawan al'umar kasar kuwa suka tsere, a cikin tsukin shekaru bakwai.

Wani bincike ya bayyana cewa yakin kasar Syria ya cinye rayukan mutane sama da dubu 350 yayin da rabin yawan al'umar kasar kuwa suka tsere, a cikin tsukin shekaru bakwai. Kungiyar nan ta Syrian Observatory for Human Rights mai cibiya a kasar Birtaniya, ta ce daga cikin wadanda suka salwanta, akwai kananan yara kimanin dubu 200 da mata sama da dubu goma 12. Akwai kuma jimillar fararen hula dubu 106 da 390 da su ma suka kasance cikin wadanda suka mutun, a wani rahoton da kungiyar ta fitar.

Gabanin yakin dai, Syriar na da yawan mutane miliyan 23 ne, inda Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane sama da miliyan shida sun fice daga kasar. A bara ma kungiyar kare hakkin jama'a ta Amnesty International ta ce kimanin mutane dubu 13 ne gwamnatin kasar ta kashe su ta hanyar rataya.