Dubban Mutane sun mutu a Turkiyya da Syria
February 6, 2023Kasashe a fadin duniya na yin gangami domin kai taimakon jinkai da ma'aikatan agaji don aikin ceto a Turkiyya da Syria inda girgizar kasar da ta auku a ranar litinin ta halaka mutane fiye da 2,500
Kasashe a fadin nahiyar Turai da Asiya da Gabas ta Tsakiya da kuma arewacin Amirka sun yi alkawarin kai gudunmawar jinkai.
Kungiyar tarayyar Turai ta aike da tawaga goma ta masu aikin ceto yayin da sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga kasashe su taimaka wa dubban iyalan da Iftila'in ya ritsa da su wadanda dama can yawancinsu sun dogara ne da tallafi.
Jamus wadda ke da Turkawa miliyan uku da ke zaune a kasar ta yi alkawarin kai agajin gaggawa.
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi alkawarin kai wa kasashen biyu tallafi a tattaunawar da ya yi ta wayar tarho da shugaban Syria Bashar al Assad da na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.
Shi ma shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce kasarsa wadda yaki daidaita a shirye take ta bada gudunmawa domin shawo kan kalubalen itftila'in.
2023-02-06T15:49:50Z UTC