Dubban masu kaura sun yi batar damo a bana | Labarai | DW | 15.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dubban masu kaura sun yi batar damo a bana

Kungiyar 'yan gudun hijira ta ce mutane 3400 sun mutu ko sun bata a kokarin tsallake iyakokin kasashen duniya baki a daya a bana.

Italien Flüchtlinge Rettung Mittelmeer

Tekun Bahar Rum tsakanin arewacin Afirka da Italiya na zama hanya mafi hatsari

Kungiyar kula da kaura ta kasa da kasa IOM ta ce a watanni biyar na farko na wannan shekara masu kaura fiye da 3400 aka yi rajistar ko dai sun mutu ko kuma sun bata a lokacin da suke kokarin tsallake kan iyakokin kasashe a fadin duniya. Kungiyar ta ce fiye da kashi 80 cikin 100 na wannan adadin sun yi kokarin shiga Turai ta teku. Adadin ya kuma haura na bara da kimanin kashi 12 cikin 100. A shekarar 2015 kungiyar ta IOM ta ce masu kaura 5400 suka mutu ko kuma aka ba da rahoton bacewarsu a duniya baki daya. Frank Laczko darektan cibiyar tattara bayanai na kungiyar IOM a birnin Berlin da ke bin diddigin masu kaura da suka bace, ya ce hanya tsakanin arewacin Afirka da Italiya ta zama mafi hatsari ga 'yan gudun hijira, inda fiye da dubu daya suka mutu a makon karshe na watan Afrilun wannan shekara.