1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Dubban bakin haure sun shiga Burtaniya

May 25, 2024

Dubban baki ne suka shiga cikin kasar Burtaniya a wannan shekarar, abin da masana ke yi wa kallon ya iya kawo nakasu ga gwamnati a muhimmin zaben da ke gabanta.

https://p.dw.com/p/4gHT1
Firaministan Burtaniya, Rishi Sunak
Firaminista Rishi Sunak na BurtaniyaHoto: Stefan Rousseau/AP/picture alliance

Sama da masu neman mafaka mutum dubu 10 suka shiga kasar Burtaniya a wannan shekarar cikin kananan jiragen ruwa, wani abu da ke nuna jan aiki da ke iya shafar Firaminista Rishi Sunak a zaben watan Juli.

A shekarar da ta gabata ne aka lura cewa adadin masu shiga kasar ta hanyar tafiyar kasada sun ragu, sai kuma ga shi sabbin alkaluma da aka wallafa a shafin gwamnti na nuna mutum dubu 10 da 170 sun kutsa kasar daga farkon watan Janairu zuwa yau 25 ga watan Mayu.

A baran dai bayanai sun nuna cewa mutum dubu bakwai da 395 baki suka shiga Burtaniyar a daidai wannan lokaci.

Firaminista Rishi Sunak, wanda ya sanar da ranar zabe a Larabar da ta gabata, ya bayyana cewa duk wani mai neman mafakar da ya shigo kasar ba bisa ka'ida ba, ya sani cewa za a aika da shi kasar Ruwanda kafin lokacin zaben.