1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar ta-baci ta jefa jama'a cikin ukuba

May 21, 2013

'Yan gudun hijirar da suka tserewa dokar ta-baci a wasu jihohin Najeriya suna fama da matsananciyar rayuwa.

https://p.dw.com/p/18bjM
Unruhe und Gewalt in Nigeria ARCHIVBILDHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

'Yan gudun hijira dake kara tserewa daga sassan jihar Borno zuwa
jihohin makobta sanadiyyar fada da ake gwabzawa na ciki halin ni ‘ya
su saboda yadda suka kasa samun matsuguni da rashin abinci da kuma
rashin samun kulawa daga Kungiyoyin bada agaji ko kuma hukumomin.
Akwai daruruwan ‘yan gudun hijira da yanzu haka ke neman mafaka a
jihohin da garuruwan dake kasashen masu makobataka da wuraren da aka
kakaba dokatar ta baci da kuma inda ake ba-ta-kashin, kuma har ya zuwa
yanzu ba su samu inda zasu zauna ba.

‘Yan gudun hijrar da suka yawancin mata ne da kananan yara sun dogara
ne ga dan taimako da wasu al'ummomi ke musu wanda kuma bai taka kara
ya karye ba abinda ya sa ake bayyana halin da suke ciki.
Na yi jin ta bakin wani da yake kan kauyukan dake kan iyakar Najeriya
da jamhuriyar Nijar wanda ya shaida min cewa yanzu haka yana cikin
daji ne ya gudu don gudun abinda ka iya faruwa da su.


"Yace yanzu haka da nake Magana da kai ina cikin daji ne mun gudu
saboda muna fargabar abinda sojoji zasu zo su yi mana don sun fara
yawo a wuraren mu mu bamu da ‘yan Boko Haram a wuraren mu yanzu haka akwai kimanin mutane dubu uku da su ka yi gudun hijira"

Red Cross
Hoto: AP

Agazawa 'yan gudun hijirar Borno da Yobe
Malam Magaji Halilu wani ne da ya tallafawa wasu daga cikin ‘yan gudun
hijirar ya kuma bayyana min irin halin da suke ciki.
Kungiyoyin bada agaji na fuskantar kalubale na samun bayanai hakikakin
inda mutanen suke abinda ke zama tarnaki ga kokarin kai musu gudumowa kamar yadda Umar Abdu Mairiga jami'in ko-ta-kwana na Kungiyar bada agaji ta Red cross ya shaida min ta wayar tarho.


"Yace a bangarenmu na Kungiyar agaji ta Red Cross muna ta kokarin
muu samu wani bayani daga rassan mu na Borno Yobe da Adamawa amma
bamu wani bayani ba sabodakatsewar hanyoyin sadarwa sai dai babban
sakatrn mu na kasa ya tafi jihar Borno jiya domin nemo bayanai kuma da
zarar mun samu zasu dauki matakin bada agaji kamar yadda muka saba.
Mun yi Magana da rassan mu dake jihohin dake makotaka da wuraren da
ake rikicin muna sauraron su bamu bayanai kan abinda ke faruwa"

Polizei in Nigeria
Hoto: Tony Karumba/AFP/Getty Images


Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun koka akan dokar ta-baci

A wani labarin kuma Kungiyoyin kare hakkin bani Adama sun fara bayyana
koke kan halin da fararen hula ke ciki a yankunan da ake gwabza fada
tsakanin Dakarun Najeriya da Kungiyar Jama'atu Ahlul Sunnan
Lidda'awati Wal Jihad wanda aka fi sani da Boko Haram musamman saboda
yadda ba'a samun labara halin da suke ciki.
Kungiyoyin sun kuma bayyana fargaba cewa jami'an tsaron Najeriya zsu
iya amfani da wannan dama wajen gallazawa fararen hula saboda ba wanda zai bada labarin abinda ke faruwa.
Wannan ma kuma shine tunanin yawancin masu gwagwarmayar kare hakkin talakawa a wannan yankin kamar yadda daya daga cikin su Comrade Garba Tela Herwagana Wudil ya shaida min.


Har yanzu dai kungiyoyin fafutukar kare hakkin bani Adama sun bukaci
kamfanonin sadarwa da su bude layukan da aka rufe domin baiwa mutane
damar jin labarin halin da ‘yan uwansu dake zaune a wadannan wuraren ke
ciki.

Mawallafi : Al-Amin Suleiman Muhammad
Edita        : Saleh Umar Saleh