Dokar kare fansho a Najeriya | Siyasa | DW | 09.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Dokar kare fansho a Najeriya

Najeriya majalisar dattawa ta amince da kudurin doka daya tanaji daurin shekaru 10 ga duk wanda aka samu da laifin sacewa ko cinye kudaden fanshon ma'aikata.

A wani sabon yunkuri na dakile masu satar kudadden yan fansho a Najeriya majalisar datawan kasar ta amince da kudurin doka daya tanaji daurin shekaru 10 a kan duk wanda aka samu da sata ko almubazarantar da kudadden 'yan fansho a kasar, abin da ya sanya kungiyoyin fafutukar tsofafin ma'aikata da ke karban fansho maida murtani.

To wannan doka da majalsair dattawan Najeriyar ta amince da ita bayan dadewar da aka yi ana jan kafa da ma matsin lamba a kan bukatar sake sabunta dokar domin kare hakokin ma'aikatan Najeriyar daga masu halin bera, da ke jefa rayuwrsu cikin mawuyacin halli bayan an gama tatse kuruciyarsu a aikin gwamnati.

Sabuwar dokar da baya ga hukuncin dauri na shekaru 10 ga duk wanda ka samu da laifin rub da ciki a kan dukiyar 'yan fansho ta ma bukaci a kwace daukacin dukiyar masu irin wannan mumunan hali. Malam Muhammad Nuarini shine sakataren kungiyar 'yan fansho ta Najeriyar, wadanda suka yi ta matsin lamba har ma da zanga- zanga zuwa ga majalisar dattawan kasar ya bayyana yadda suka ji da samun wannan doka.

‘' Ai muna cikin murna da wannan doka da 'yan majalisa suka kadammar domin mun dade muna fafutukar a nuna gaskiya da adalci a kan abinda ya shafi kuddadden 'yan fansho a Najeriya wadanda suka kai suka kawo a wajen aikin kuma yanzu sun zama gajiyayyu a cikin kasa. Don haka 'yan majalisu sun yi abinda ya kamata kuma wanda suka yi daga baya dole wannan ya shafe su''.

Koda yake sabuwar dokar da ta kama hanyar maye gurbin wacce ake da ita tun 2004 ta samar da tanaji na cin gajiyar kudin fansho ga dukkanin ma'aikatar da ke da mutanen da suka kai uku da ke aiki a karkashinta a Najeriyar, domin kare hakokin kanana ma'aikata da ake masu kwange a cikin kasar, amma ga Malam Sani Aliyu na kungiyar fafautukar yaki da cin hanci da tabbatar da gaskiya na mai tababar tasirin da zata yi.

‘'Rashin imani da rashin tausayi da ma rashin sanin ya kamata shi yasa ake taba kudadden mutanen da suka tsara rayuwarsu suka yiwa kasa aiki watau ‘yan fansho. To sai dai ba sa dokar bane, aiwatar da ita shine matsala a nan, ai a baya akwai dokoki da dama da aka tsara a kan wanda aka samu ya aikata hali irin wannan na satar kudaden 'yan fansho amma ana mafani da shi?''

A lokutan baya dai majalisar datawan Najeriyar ta yi ta ihun daya kama hanyar zama na banza a kan mutanen da aka zarga da yin ba dai-dai ba a harakar kudaden fansho, wadanda suka yi biris da gayyaratar da ta yi masu saboda zargin suna samun kariya daga gwamnati, Amma ga Sanata Kabiru Gaya na kwamitin kula da harkar fansho a majalisar ya bayyana cewa.

"Juyawar da masu tafka cin hanci da rashawa da ma sata irin ta bera da tsakar rana suka yin a afkawa kudadden yan fansho da kiyasin ya nuna sun yi gaba da kusan Naira bilyan 400 ya jefa rayuwarr yan fansho cikin ni yasu inad sukan yi ta layi don karabar hakokinsu, duk kuwa da sauye-sauyen da gwamnati ke yin a kafa hukuma ta musamman mai kula da lamarin.

Sauti da bidiyo akan labarin