1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Diyya ga wadanda zanga-zanga ta shafa

Abdoolaye Mamane Ahmadou
February 3, 2015

Hukumomin Nijar sun girka wani kwamitin da zai sake inganta wuraren ibada da gidajen mabiya addinin kirista da zanga-zangar adawa da mujallar Charlie Hebdo ya janyo

https://p.dw.com/p/1EV1j
Niger Proteste gegen Mohammed Karikaturen in Charlie Hebdo 16.1.2015
Hoto: STR/AFP/Getty Images

Wuraren ibada da makarantu da ma gidajen marayu na mabiya addinin kirista da dama ne suka tabu a yayin zanga zangar inda kawo yanzu wasu kiristocin ke ibadansu a karkashin runfuna a garuruwan Yamai da Birnin Damagaram. Rikicin na ranar 16 da 17 da wasu matasan musulmin kasar ta Nijar suka yi dai ya rutsa ne da kimanin sama da kiristoci 360 a garuruwan Zinder da birnin Yamai, inda matasan a fusace suka toye wasu majami'u 73 tare da bannata makarantu da wasu gidajen marayu da dama a yayin zanga-zangar ta birnin Yamai da yankin Damagaram.

A cikin wani yanayi na juyayi da tallafawa dai ne gwamnatin ta kafa wani kwamitin da ke bin diddigin matsalolin da kiristocin suka riski kansu a ciki. Matakan kuwa da kwamitin ya dauka dai sun hada da tallafawa mabiya addinin kirista domin sake gina ko gyara wuraren ibadar su da na kwanciyar da zanga-zangar ta rutsa da su Mme Kane Aichatou Boulama ita ce daraktar fadar Frayministan kasar Nijar kuma shugabar kwamitin

Niger Proteste gegen Mohammed Karikaturen in Charlie Hebdo 16.1.2015
Mutane da dama sun rasa muhallensuHoto: STR/AFP/Getty Images

"Gwamnati ta dauki mataki za ta kama a yi wa mutanen nan gyare- gyaren wurarensu da gidajensu da wuraren ibadarsu, yanzu maganar ga da ni ke an fara aune-aunen wuraren da za'a aikin nan sa'an nan gwamnati zata ci gaba da agazawa wadanda basu da gidaje abin da ya shafi abinci kuma za'a ci gaba kama masu hakan yara da anka konewa gidajen daukar karatu ko anka konewa kayan karatunsu zamu i gaba da taimakawa aiki ne mun shiga ciki zamu ci gaba da yi kuma zamuyi shi fisabilillahi"

Wadanda harin ya shafa sun yaba da yunkurin gwamnati

Tuni dai kirstocin kasar ta Nijar da ke da wakillai a cikin kwamitin suka gamsu da yanda kamitin ya ke tafiyar da ayukansa tare da nuna goyon bayansu ga duk wasu hanyoyin da gwamnatin take son dauka domin inganta rayuwar mabiya addinin na kirsita a jamhuriyar Nijar Fasto Sumaila Labo na daya daga cikin mambobin kwamitin, daya daga cikin fastocin da aka konawa wurin ibada da gidansa a Eglise Evangelique da ke unguwar bukuki ta biyu a birnin Yamai.

Frankreich Niger Präsident Mahamadou Issoufou in Paris bei Francois Hollande
Hoto: M. Alexandre/AFP/Getty Images

"Zancen matakin farko gwamnati ta yi duk kokarinta domin ganin wadanda ba su da gidaje ko wurin kwana an samar masu da wuraren kwanciya to amma har yanzu akwai bukatu mun gamsu da matakin farko to amma kuma muna jiran mataki na biyu da mataki na uku muna godiya da yanda aka dauki wadannan matakan da kuma yanda muka yi aiki a cikin wannan kwamitin cikin sakewa da fahimtar juna tsakanin mambobi"

A yanzu hakan dai kwamitoci da dama ne ke ci gaba da gudanar da ayukka tukuru domin kara kyautata al'amura ga mabiya addinin kiristan biyo bayan wata ganawa da Firaminista da ma shugaban kasar Nijar Alhaji mouhamadou Issoufou ya yi da su, to amma sai dai wasu masu nazarin al'ammuran na ganin abin jira shi ne bin diddginin aiyukkan kwamitocin domin ganin an zartar da shwarwarin da suka bayar.