Dawo da hukuncin kisa a kasar Chadi | Labarai | DW | 31.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dawo da hukuncin kisa a kasar Chadi

Gwamnatin kasar Chadi ta sake dawo da yanke hukuncin kisa ga masu manyan laifuka watanni shida bayan soke hukuncin a kasar.

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby

Hakan dai ya biyo bayan amincewa da 'yan majalisun dokokin kasar suka yi da wata sababbin tsauraran dokoki na yaki da ta'addanci sakamakon hare-haren da kasar ke fuskanta daga kungiyar Boko Haram da ta addabi Najeriya da makwabtanta. Tun dai bayan da aka fuskanci munanan tagwayen hare-haren kunar bakin wake a N'Djamena babban birnin kasar, mahukuntan na Chadi suka sake daukar kwararan matakan tsaro, da suka hadar da soke amfani da Hijabi da kuma barace-barace. Sai dai 'yan adawa da kuma kungiyoyin masu fafutuka na nuna fargabarsu ga sababbin dokokin da gwamnatin ta kafa da suke cewa za su iya take hakkin dan Adam a kasar. A hannu guda kuma baya ga hukuncin kisa ga wadanda suka aikata manyan laifukan ta'addanci majalisar ta mayar da hukuncin masu kananan laifukan ta'addancin daga shekaru 20 zuwa daurin rai-da-rai.