1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Daruruwan baki sun fice daga Gaza

November 2, 2023

Daruruwan baki 'yan kasashen waje ne suka samu ficewa daga Gaza i zuwa kasar Masar, inda Amurka ke tabbatar da wasu gomman 'ya'yanta a ciki.

https://p.dw.com/p/4YLNP
Yadda baki ke ficewa ta mashigar Rafah
Yadda baki ke ficewa ta mashigar Rafah Hoto: Arafat Barbakh/REUTERS

Kimanin wadanda ke rike da fasfo na kasashen ketare mutum 400 ne suka fice daga Gaza, ta mashigar nan ta Rafah i zuwa kasar Masar, kamar dai yadda kamfanonin dillancin labarai daban-daban suka ruwaito a wannan Alhamis.

Haka nan ma akwai karin wasu gomman marasa lafiya da sauran wadanda suka jikkata a yakin Isra'ila da Hamas da ke kan hanyar biyowa ta mashigar.

Shugaban Amurka Joe Biden ya tabbatar da kasancewar Amurkawa 74 daga cikin wadanda suka fitan.

Wannan ne rukuni na biyu na baki 'yan kasashen ketaren da ma wasu da ke da fasfo din Falasdinu da ke samun damar fita daga Zirin na Gaza zuwa Masar.

A ranar Laraba ne aka bude mashigar ta Rafah tun bayan hari da kungiyar Hamas ta kaddamar a Isra'ila a ranar bakwai ga watan jiya, harin da ya janyo ramuwar gayya da ake ciki.

Ma'aikatar kula da al'amuran kasashen waje na Masar, ta ce za ta taimaka wajen ganin an kwaso 'yan kasashen waje akalla dubu bakwai daga Gazar.