Dangote zai zuba jarin dala biliyan daya a Zimbabuwe
November 12, 2025
Rukunin kamfanonin Dangote na Najeriya zai zuba jarin akalla dalar Amurka biliyan guda a fannin gina bututun mai, da samar da wutar lantarki da kuma masana'antar siminti a Zimbabuwe, in ji jagoran kamfanin Aliko Dangote.
Dangote, wanda ya fi kowa arziki a Afirka, ya gana da shugaban kasar Zimbabuwe Emmerson Mnangagwa, inda bangarorin biyu suka sanya hannu kan yarjejeniyar zuba jari da gwamnati a yau Laraba.
A baya dai hamshakin dan kasuwar ya taba ziyartar Zimbabuwe a shekarar 2015, a zamanin marigayi Shugaba Robert Mugabe wanda Mnangagwa ya gaji kujerarsa bayan juyin mulkin 2017, amma ya yi watsi da shirin zuba jari a kasar da ke kudancin Afirka saboda dalilai marasa tabbas.
Dangote yana da kamfanoni a kasashe 17 na Afirka kuma daya daga cikin rassansu da ke sarrafa siminti na jagorantar dukkan masana'antun yin siminiti na nahiyar.