1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dandalin Matasa: Matasa da wasannin motsa jiki

Binta Aliyu Zurmi AH
April 1, 2021

Shirin Dandalin Matasa(01-04-21) ya duba yadda matasa ke rungumar wasannin motsa jiki a Najeriya tare da amfanin da damar domin samun horo don rage yawan gararranbar matasan marasa aiki a kan tittuna.

https://p.dw.com/p/3rUHZ

Matasa da sune ginshikin al'umma, kuma a kasashen Afirka sun fi kaso 70 na yawan al'ummar da ke wannan nahiyar kuma kaso mai yawa daga cikinsu ba su da ayyukan yi.To sanin kowa ne dai matasa da dama sun kasance masu sha'awar wasannin motsa jiki kama daga wasan kwallon kafa da na kwallon kwando gami da guje-guje. Hakan ya sa wani matashi a Jihar Bauchin Yakubu mai suna Babayo Liman kuma tsohon dan kwallon kafa wanda har ya kai matakin wakiltar Najeriya a rukunin 'yan wasa na kasa da shekaru 20 ya bugi kirji ya bude filin wasan kwallon kafa na zamani da ya sa wa suna Babayo Liman Arena, wanda ke samun halarta dimbin matasa daga lungu da sako na jihar.