Dandalin Matasa: 05.03.2026
March 12, 2026
Talla
Gwamnatin jihar Sokoto ta ware naira biliyan don aikin ciyarwa a azumin Ramadanan bana 2026, kuma tuni matasa suka fara dandazo a wuraren da ake aikin rabon abincin a ko wace rana. A lokacin da aka fara azumin na bana gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya yi kira ga masu hannau da shuni a jihar su taimaka wajen cikyar da mabuƙata ganin yadda matasa da dama da kuma gajiyayyu ke amfana da hakan.