1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Dan majalisar Najeriya na shan sukar aurar da 'yan mata 100

May 17, 2024

A Najeriya ana ci gaba da maida martani kan takaddamar da ta kaure tsakanin majalisar dokokin jahar Naija da ma'aikatar kula da mata da kananan yara, kan yunkurin kakakin majalisar na aurar da marayu mata 100.

https://p.dw.com/p/4fxl0
Hotunan wasu 'yan matan Chibok da aka kubutar da su daga hannun Boko Haram a  Najeriya
Hotunan wasu 'yan matan Chibok da aka kubutar da su daga hannun Boko Haram a NajeriyaHoto: Sunday Aghaeze/AFP

Kakakin majalisar Abdulmalik Sarkindaji, ya kekesa-kasa kan cewa ya yi hakan ne domin ya taimaki al'ummar  da yake wakilta, domin su ci gaba da gudanar da kyakkyawar rayuwa, matakin da ministar al'amuran matan Najeriyar Uju Kennedy-Ohanenye, ta yi kakkausar martani kan matakin inda take cewa an tilasta musu kuma wasu basu kai munzalin yin aure ba.

Karin bayani: Sojojin Najeriya sun zubar wa mata 10,000 juna biyu 

Ba sabon al'amari bane gangamin aurar da mata a lokaci guda a tarayyar Najeriya musamman a shiyyar arewacin kasar, inda ko a watan Janairun wannan shekara dan majalisar dokokin kasar daga jihar Borno Muktar Aliyu Betara, ya aurar da mata 180 da Boko Haram suka hallaka iyayensu.

Karin bayani: Nijar: Damuwa kan yawan mutuwar aure

Kazalika a shekarar da ta gabata gwamnatin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta aurar da mata 1,800 a wani shiri da ta yi wa lakabi da auren-gata.