Dalilan kin sakin Dasuki da El-Zakzaki | Labarai | DW | 23.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dalilan kin sakin Dasuki da El-Zakzaki

A karon farko tun bayan garkamesu a gidan yari ba tare da beli ba, gwamnatin Najeriya ta bayyana dalilan ci gaba da tsare tsohon mashawarcin tsaro Kanal Sambo Dasuki mai ritaya da shugaban 'yan Shi'a Ibrahim El- Zakzaky.

Gwamnatin Najeriya ta ce bata da niyayr musgunawa El-Zakzaky da ake cigaba da tsarewa a Abuja. Sai dai kuma tana bashi kariya daga barazanar da ke iya tashi sakamakon samun 'yancinsa, a yayin da Col Sambo Dasuki ke jerin shari’un da gwamnatin kasar.

Malam Garba Shehu, kakakin gwamnatin ya ce Abuja zata Amince da 'yancin na Dasuki ne kawai in har an kai ga kammala daukacin shari’un da ke gabansa a halin yanzu.

Jerin kotunan Najeriya dama na wajen kasar da suka hada da ita kanta kotun yankin yammacin Africa  sun nemi sakin na col Dasuki da ake zargi da almubazzaranci da kudin yaki da ta’addanci kusan Dala miliyan dubu biyu da dari daya.