Dalibai sun mutu bayan hari a Najeriya | Labarai | DW | 06.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dalibai sun mutu bayan hari a Najeriya

Wani hari da ake zargin masu kishin Islama da aiwatarwa ya hallaka kusan dalibai 30 a arewacin Tarayyar Najeriya.

Masu kaifin kishin Islama sun hallaka dalibai 29 da malamin makaranta daya a yankin arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya. Kuma yanzu haka ana jinyar wasu daga cikin daliban da suka samu raunuka sakamakon harbin bindiga.Maharan sun kona wasu daga cikin daliban, yayin harin na sanyin safiyar wannan Asabar, a makarantar kwana ta 'yaran maza da ke garin Mamudo na Jihar Yobe.

Hare-haren na masu kaifin kishin addinin Islama da ake dangantawa da kungiyar Boko Haram tun cikin shekara ta 2010, sun yi sanadiyar halakar dubban mutane,-abin da ya sa gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kafa dokar ta-baci cikin wasu jihohi uku na yankin arewa maso gabashin kasar.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas