1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Dalibai 6 sun mutu a hannun 'yan bindiga

Ramatu Garba Baba
August 24, 2021

'Yan bindiga sun ce dalibai 6 sun mutu a hannunsu a yayin da suka nemi a biya su kudin fansa kafin su saki sauran daliban Islamiyyan Tegina da suka yi garkuwa da su.

https://p.dw.com/p/3zPHc
Suche nach rund 200 entführten Kindern in Nigeria
Hoto: Mustapha Gimba/AP Photo/picture alliance

Rahotanni daga Najeriya na cewa, dalibai shida sun mutu a hannun 'yan bindigan da suka yi garkuwa da su, suna daga cikin dalibai 136  da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su, daga wata makarantar Islamiyya da ke garin Tegina a jahar Neja. Suna daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su tun a watan Mayun wannan shekarar ta 2021.

A wani karin bayani da yayi ma kamfanin dillancin labarai na Reuters, Abubakar Garba Alhasan, wanda shi ne shugaban makarantar da aka sace daliban, ya ce, 'yan bindigan sun sheda masa cewa, yaran sun mutu ne bayan sun sha fama da rashin lafiya. Ya kara da cewa, sun nemi a biya su kudin fansa, don amso sauran daliban da ke hannunsu.