Dakon sakamakon zaɓe a Kenya | Labarai | DW | 08.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakon sakamakon zaɓe a Kenya

Hukumar zaɓen Kenya ta ce zata sanar da sakamakon zaɓe ran juma'a sai dai masu sanya ido kan yadda abubuwa ke gudana na shakkun ko hakan zai faru

Har yanzu dai al'ummar Kenya na dakon sakamakon zaɓen ƙasa, inda Uhuru Kenyatta wanda ke shan gaba ke kallon yawan ƙuri'unsa suna reto kusa da makin na kashi 50 cikin 100, ake kuma ƙiyasta yawan a kan kashi 49 da ɗigo 93 cikin 100.

A yanzu haka dai an ƙidaya kashi 90 cikin 100 na ƙuri'un. Samun kashi 50 cikin ɗari na da mahimmanci sosai ga Kenyatta dan ta haka ne kaɗai zaɓen ba zai je zagaye na biyu ba.

A wannan juma'ar ce hukumar zaɓen ta sanar da cewa zata kammala kiɗanya ƙuri'un to amma har yanzu waɗanda ke sanya ido kan yadda abubuwa ke gudana na shakkun ko hukumar zata cika alƙawarinta na fidda sakamakon a cikin wannan daren. Kawo yanzu dai ƙasashen yamma sun yi gargaɗin cewa dangantakarsu da Kenya zata sha wuya idan har Kenyatta ya yi nasara.

A wani labarin kuma, Kotun hukunta manyan laifukan yaƙi ta ICC ta ɗage shari'ar ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a Kenya William Ruto zuwa ranar 28 ga watan Mayu idan Allah ya kai mu, bayan da lauyoyinsa suka yi ƙorafin rashin isashen lokacin gudanar da shirye-shiryen da ya kamata kafin shari'ar. William Ruto wanda ake tuhuma da haddasa rikicin da ya kai ga hallakar mutane dubu ɗaya da ɗari biyu bayan zaɓen da aka yi a ƙasar a shekarar 2007 shine abokin takarar Uhuru Kenyatta ɗaya daga cikin manyan 'yan takaran shugaban ƙasa.

Shima Kenyatta wanda ake zargi da aikata laifuka irin na Ruto, ya sami labarin cewa shima an ɗage nasa shari'ar a Kotun ta ICC zuwa watan Yuli.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammed Awal Balarabe