1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Martani kan dakatar da shirin sufurin sama

Uwais Abubakar Idris
September 20, 2018

A Najeriya kwararu a fanonin sufurin jiragen sama na cigaba da tsokaci kan matakin gwamnati na dakatar da batun kafa sabon kamfanin jiragen sufurin sama da illar da zai iya yi ga wannan sashi a kasar.

https://p.dw.com/p/35FLO
Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

To haka kwatsam ne dai gwamnatin ta bada wannan sanarwar a ta bakin ministan kula da sufurin jiragen saman kasar Sanata Hadi Sirika, wanda ya ce an dakatar da kafa kamfanin bisa dalilai na tsare-tsare da dabaru. Abinda ya jefa tambayoyi don sanin shin a zahiri mai ya faru ne.

Watani biyu ne dai da ministan ya sanar da kafa kamfanin a aikin da ya lakume makudan kudadde, bisa alkawarin cewa jirgin saman sabon kamfanin zai sheka a guje ya tashi a watan Disambar bana, amma maimakon haka sai dakatarwa ta biyo baya.

Alamu da ke nuna akwai dai miskilar da aka samu, domin an tsara kashi casa'in na kamfanin ya kasance hannun ‘yan kasuwa ne. Captain Muhammad  Bala Jibril tsohon darakta ne a ma'aikatar sufurin jiragen  saman Najeriyar, ya ce tun farko sun ja hankalin gwamnati da shawarar da suka bayar.

Dakatar da wannan shiri na kafa kamfanin jiragen saman Najeriyar babban al'amari ne musamman ganin irin dokin da al'ummar kasar suka nuna saboda dadewa su na neman kaiwa ga hakan.

Amma kwararru masu zuba jari sun dade da nuna ‘yar yatsa a farkon tsarin da aka yi, abinda ya sanya Mallam Yusha'au Aliyu masani a fanin tattalin arziki da zuba jari bayan cewa sun hango mishkila da dadewa.