Cutar Lassa ta halaka mutum 110 a Najeriya | Labarai | DW | 06.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cutar Lassa ta halaka mutum 110 a Najeriya

Cibiyar da ke yaki da bazuwar cututtuka ta NCDC a Najeriya, ta ce zazzabin Lassa ya lakume rayukan mutane dari da goma a farkon wannan sabuwar shekarar.

Alkaluman da cibiyar ta fitar a wannan Talata ta ce shi ne mafi yawa da ke nuna barnar da cutar ta haddasa tun bayan na shekarar 2016.

Cibiyar ta ce an tabbatar da bullar cutar a jihohi goma sha takwas na kasar. Ministan lafiya Isaac Adewole ya shaidawa manema labarai cewa, ana gab da samar da maganin riga kafi don dakile yaduwar cutar mai saurin kisa.

Hukumar Lafiya ta Duniya a na ta bangaren, ta ce annobar ta zarta tunani ganin a wasu wuraren gwaje-gwajen cutar sun nuna yadda take yaduwa da kuma tabbatar musu da mutuwar mutane saba'in da biyu.