Cutar Ebola ta hallaka mutane a Saliyo | Labarai | DW | 26.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cutar Ebola ta hallaka mutane a Saliyo

Rahotannin daga kasar Saliyo na cewar mutane hudu sun rasu sakamakon kamuwa da kwayar cutar nan ta Ebola mai saurin hallaka mutane.

Jami'an kiwon lafiya a kasar yanzu haka na cigaba da gudanar da bincike kan yankin da aka samu bullar cutar da ma dai inda mutanen suka rasu ko ya Allah za a samu karin wanda ke dauke da kwayar cutar don killace su kafin su kai ga yada ta.

A makonnin bayan ne dai aka samu bullar wannan cutar ta Ebola a yankin yammancin Afirka inda aka samu rasuwar mutane da dama a Gini Konakry, al'amarin da ya sanya kasar rufe iyakokinta da makotanta don gudun bazuwar kwayar cutar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal