1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COVID-19 na ci gaba da yaduwa a duniya

May 18, 2020

Sama da mutum miliyan hudu da dubu 800 ne a halin yanzu ke dauke da kwayar cutar corona a fadin duniya, cutar da alkaluma ke cewa ta hallaka wasu sama da dubu 310.

https://p.dw.com/p/3cNVC
Krankenhaus China Wuhan
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Bohan

Kididdigar da jami'ar Johns Hopkins ta Amikra ke fitarwa a kullum, ta ce mutane sama da miliyan da dubu 800 ne suka warke daga wannan cuta ta sarkewar numfashi.

A lissafin wannan jami'a dai, annobar ta COVID-19 ta karade kasashe da kuma yankunan duniyar 210, tun bayan bullar ta cikin watan Disambar bara a yankin Wuhan na kasar China.

Kasar Amirka ce ke gaban kowace kasa ta duniya da yawan wadanda ta kama ya zarta miliyan daya da dubu 500, ta kuma kashe sama da mutum dubu 90 a yanzu.

Kasa ta biyu ita ce Rasha da wadanda suka kamu a yanzu suka doshi dubu 300 sai Spain da Birtaniya da kuma Brazil.

Nahiyar Afirka na da adadin wadanda suka kamu dubu 86,381, inda Afirka ta Kudu ke kan gaba Masar ke biye mata.

Najeriya mai yawan al'uma a nahiyar na da mutum dubu 5,959 da suka kamu.