COVID-19: An dage wasannin Olympics | Labarai | DW | 24.03.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

COVID-19: An dage wasannin Olympics

Fraministan Japan Shinzo Abe ne ya nemi shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na kasa da kasa Thomas Bach da ya dage gasar, saboda karuwar yaduwar cutar Coronavirus.

Matakin ya biyo bayan karin matsin lamba kan bukatar dage wasannin motsa jikin da ya kamata a gudanar a birnin Tokyo, saboda annobar Coronavirus din da ke neman mamaye duniya baki daya.

Tuni kasashen Kanada da Ostraliya suka ce ba zasu aike da 'yan wasansu zuwa Olympics da aka tsayar da farawa a ranar 24 ga watan Yulin wannan shekarar ba.