1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma Francis ya nemi kasashen duniya su hada kai

Abdoulaye Mamane Amadou
April 12, 2020

Babban limanin darikar Katholica na duniya Paparoma Francis yayi jawabinsa na bukin Ista ko Paques, tare da neman ganin kasashen duniya sun hada kai don yakar cutar coronavirus.

https://p.dw.com/p/3ao6P
Papst Franziskus  Messe Ostern Vatikan
Hoto: Getty Images/A. Solaro

Paparoma Francis ya yi kira da a soke basusukan da ake biyar kasashe matalauta da kuma yin sakin mara ga matakan takunkumi na kariyar tattalin arziki da ake kakaba wa wasu kasashen da jagoran darikar ta Katholika ya kira da cewa suna matukar kokarinsu wajen ganin sun kawo dauki ga jama'a,inda ya ce duba da halin da ake ciki a yanzu ya kamata kasashen duniya su sassauta takunkuminsu ga kananan kasashe.

Kana kuma babban limamin ya kuma a kira ga ksashen duniya da su hada kansu wuri daya domin yakar cutar annobar coronavirus da ke ci gaba da yin ta'adi a fadin duniya, tare da nanata kirana ga kasashen duniya da su tsakaiga wuta, yana mai cewa ba a yanzu ba wai lokaci ba ne na yin hkan domin kuwa kudaden da ake zubawa ana kera makamai ka iya taimakawa wajen ceto rayukan jama'a.