1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COVID-19: Arzikin Nijar ka iya rauni

Salissou Boukari LMJ
April 2, 2020

Wani hasashe da aka yi kan matakan da gwamnatin Jamhuriyar Nijar ke dauka sakamakon cutar Coronavirus, na nuni da cewa kasar da ke daga cikin kasashe mafi talauci a duniya za ta fuskanci koma bayan tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/3aNkS
Symbolbild Corona-Virus Impfstoff
Annobar Coronavirus ta addabi duniyaHoto: picture-alliance/dpa/Geisler-Fotopress

Hasashen dai ya nunar da cewa Nijar din ka iya fadawa cikin halin tsaka mai wuya na tattalin arziki cikin wannan shekara ta 2020 da muke ciki. Kawo yanzu dai mutane 70 ne aka tabbatar suna dauke da kwayar cutar ta Coronavirus da suka hadar da maza da mata da kuma matasa a kasar.

Cutar ta bulla a wasu jihohin

Bayan birnin Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar ta Nijar, inda ake ganin nan ne kawai cutar an kuma samu wasu mata biyu a birnin Maradi da ke gabashin kasar da suma ke dauke da cutar. 

Krankenhaus in Niamey, Niger
Kimanin mutane 70 sun kamu da Coronavirus a NijarHoto: NigerInter.com

Shi ma dai gwamnan jihar Dosso ya sanar da cewa wani dan kasar da ya fito daga birnin Lagos na Tarayya Najeriya na dauke da wannan cuta bayan da akayi masa gwaji a garin Junju na gundumar Gaya da ke cikin jihar ta Dosso. An kuma bayyana cewa kimanin mutane biyar ne aka tabbatar sun rasa rayukansu a Jamuhuriyar ta Nijar sakamakon wannan cuta. 

Gwamnati za ta bayar da tallafi

Ana dai ganin matakan hana zirga-zirga da mahukuntan kasar ke dauka domin dakile yaduwar cutar, za su iya hana hada-hadar kasuwanci na cikin gida da ma na kasa da kasa. Wannan ne ya sanya ake hasashen bunkasar tattalin arzikin kasar ta Nijar zai fadi kasa daga kaso sama da shida cikin 100 zuwa kasa da kaso biyar cikin 100 kaman yadda ministan kudi na Jamhuriyar ta Nijar Mamadou Diop ya sanar. Gwamnatin ta Nijar dai ta sanar da daukan tarin matakai na tallafawa al’ummar kasar sakamakon hana su fita da aka yi saboda cutar ta Coronavirus. Sai dai tuni kamfanonin kasar suka fara ji a jikinsu.