1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cinikin makamai tsakanin Rasha da Iraƙi

November 10, 2012

Mahukuntan Iraƙi sun ce sun soke wata yarjejeniya ta sayen makamai ta dalar Amurka biliyan huɗu da kusan rabi da su ka sanya hannu su da takwarorinsu na ƙasar Rasha.

https://p.dw.com/p/16gZM
Hoto: AP

Firaministan Iraƙi Nuri al-Maliki ne ya sanar da janye yarjejeniyar bayan da ya dawo daga wata ziyara da ya kai Moscow dangane da cinikin makaman inda ya ce Bagdad ta sauya ra'ayinta game da cinikin saboda ɗumbin rashin gaskiyar da ke tattare da shi musamman ma dai batun cin hanci da rashawa.

Tuni dai firaminista al-Maliki ya ce sun ƙaddamar da bincike kan sha'anin sai dai bai yi ƙarin haske game da takamaiman wanda za a bincika ba kamar yadda kakakinsa Ali Mussawi ya shaidawa manema labarai.

Kawo yanzu dai mahukuntan Moscow ba su ce uffan ba game da wannan batu, wanda ke zaman babban koma baya garesu na yunƙurin da su ke wajen faɗaɗa ƙarfin ikonsu na cinikin makamai a yankin gabas ta tsakiya.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Halima Balaraba Abbas