Cin zarafin firsinoni a Najeriya | Siyasa | DW | 18.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Cin zarafin firsinoni a Najeriya

Jami'an tsaron na gana wa firsinoni azaba da suka hada da cire musu hakora da farce, sannan da yi musu bulala da wayoyin karfe tare kuma da amfani da wutar lantarki.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana hakan ne a cikin wani rahoton da ta wallafa baya-bayan nan mai taken "Barka da zuwa Jahannama, cin zarafi a tsarin tsaron Najeriya".

"An daure hannaye na biyu da kafafuwana ta baya. Sun yi mini dan karen duka da karfe, da kuma katako. Amma mafi radadi shi ne rataye ni da suka yi kafa ta a sama, kai na a kasa tsawon awa daya."

Wannan dai Onyekachi kenan dan shekaru 33, yana shaida wa tashar DW halin da ya shiga a hannun 'yan sanda a jihar Imo da ke kudancin Tarayyar Najeriya. Cin zarafi da gana wa mutane azaba, ya zama ruwan dare a tsakanin 'yan sanda da ma sojojin Najeriya, inji kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnmesty International.

Netsanet D. Belay Amnesty International

Netsanet D. Belay na kungiyar Amnesty International

Netsanet Belay shi ne daraktan sashen kula da nahiyar Afirka a kungiyar ta Amnesty inda yake cewa.

"Mun gano cewa azabatarwa ta zama abin yau da kullum da 'yan sanda ke amfani da ita lokacin bincikensu a kokarin matsayawa wadanda ake zargi da su amsa laifinsu. Ya zama ruwan dare tsakanin jami'an 'yan sanda."

Tsawon shekaru bakwai Amnesty ta yi nazarin bayanan shaidun ganin ido kuma tsoffin firsinoni fiye da 500 da danginsu. Sun tattara sahihan bayanai daga lauyoyi sannan ita kanta kungiyar ta tura masu sa ido a gidajen kurkukun Najeriya. Daga cikin matakan azabtarwar, har da cire wa tsararrun hakora da farce da karfi, bulala da karfe da katako. A wani lamarinma, akwai wata mata da aka fesa mata hayaki mai sa hawaye a farjinta, inji Netsanet Belay:

"Mun kuma tattara bayanai na cin zarafin mata. Akwai wasu matan da aka fesa musu sinadarin kashe gobara a gabansu, a kokarin tatsar bayanai daga wurinsu. Mun ga nau'in azabatarwa mafi muni a Najeriya."

Amnesty International - Welcome to hell fire

"Barka da zuwa Jahannama" - Amnesty International

An yi kiyasin cewa mutane kusan 10000 aka kame a yakin da sojojin Najeriya ke yi da mayakan Boko Haram. Sai dai kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce sau tari zargin da ake yi bai taka kara ya karya ba, kuma wadanda a kan kama sukan bata a bayan kanta.

Amnesty ta kara da cewa mafi yawancin lokuta ba a hukunta masu cin zarafin firsinoni, kana ba bu mai tunanin biyan wadanda abin ya shafa diyya. Saboda haka Amnesty ta yi kira da a kawo karshen wannan al'ada ta rashin bin doka. Ko da yake an gabatar wa majalisar dokokin Najeriya wani shirin doka da ya tanadi hukunta masu azabatar da firsinoni, amma har yanzu ba a rattaba wa dokar hannu ba.

Sauti da bidiyo akan labarin