Ci gaban kone kone a kasar Faransa | Labarai | DW | 14.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban kone kone a kasar Faransa

A Fransa har yanzu da sauran rina kaba wajen magance kone konen motoci da masu zanga zanga ke yi a kayuka daban daban na wannan kasa.

A dare na 17 na wannan tashe tashe hankulla, an kona motoci 271.

To saidai akwai alamun samun rangwame idan a ka kwatanta da yawan motocin da ka kona a lokkatan da su ka gabata.

Tsakanin daren jiya zuwa sahiyar yau litinin jami´an tsaro sun capke a kalla, mutane 112 da a ka samu da hannu a cikin wannan aika aika.

Yau ne a ke sa ran dokar ministan cikin gida, ta kora bakin da ke da hannu a ciki, daga kasar Fransa.

Daga jimmilar mutane 2652 da a ka kama, an yanke wa 375 hukuncin zama gidan kurkuku.

Shugaban hukumar zartaswa ta kungviyar gamayya turai Jose Manuel Barroso ya sannar cewa kungiyar zata tallafawa Fransa da kudade Euro million 50, don rage assarorin da ta yi a cikin kone konen, wanda jimmilar su ya zuwa yanzu, su ka tashi Euro million 200.