Ci gaba da zaman makoki a Faransa | Labarai | DW | 18.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da zaman makoki a Faransa

An yi shiru na minti guda a birnin Nice na kasar Faransa, domin tunawa da mutanen da suka rasa rayukansu yayin wani hari da aka kai da babbar mota a lokacin bikin tunawa da ranar juyin-juya halin kasar.

Zaman makoki a Faransa

Zaman makoki a Faransa

Mahukuntan kasar ta Faransa dai sun tabbatar da mutuwar mutane 84 yayin da wasu da dama suka jikkata. Dubun-dubatar mutane ne dai suka halarci wajen zaman makokin trae da yin shiru na minti guda da aka gudanar a birnin na Nice da kuma wasu sassan kasar ta Faransa. A yayin da ya isa birnin na Nice, Firaministan Faransa Manual Valls ya fuskanci fushin al'ummar da suka halarci zaman makokin, inda suka yi tai masa ihu tare da kiran ya sauka daga kan mukaminsa. Kawo yanzu dai masu binicike na kasar ta Faransa basu kai ga gano ko maharin na birnin Nice mai kimanin shekaru 31 a duniya, Mohamed Lahouaiej-Bouhlel dan asalin kasar Tunusiya na da alaka da kungiyar 'yan ta'addan IS ba, yayin da tuni kungiyar ta dauki alhakin kai harin.