Ci gaba da yaki da Ebola | Labarai | DW | 17.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da yaki da Ebola

Al'umomin kasa da kasa suna ci gaba da yin aiki tukuru domin dakile cutar Ebola mai saurin kisa da ke addabar yammacin Afirka.

Likitan nan dan kasar Amirka da ya sha da kyar daga annobar cutar Ebola Dr. Kent Brantly ya ce bai kamata a tsaya bata wani dogon lokaci ba a yakin da ake ci gaba da yi domin dakile yadda cutar Ebola ke saurin lakume rayukan al'umma. Brantly ya shaidawa majalisar dattawan Amirka cewa ba abu ne da za a bata watanni ko makwanni ba wajen ganin an dauki kwakkwaran mataki a kai. Batun nasa dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da shugaban Amirkan Barack Obama ya sanar da wasu manufofi na yakar cutar Ebolan da ya bayyana da barazana ga duniya. Oabama ya kuma ba da umurnin tura dakarun Amirkan har 3,000 zuwa kasashen yankin yammacin Afirka da ke fama da wannan annobar tare da bada horo ga jami'an lafiya. Wannan shirin dai an kiyasta cewwa zai lakume kimanin kudi dalar Amirka biliyan daya.