Ci gaba da kai hari yankin Niger Delta | Labarai | DW | 07.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da kai hari yankin Niger Delta

Kungiyar mayakan sakai ta Niger Delta Avengers ta tsame hannunta a zargin da ake cewa ita ta kai hari a kan bututun mai mallakar kamfanin hakar albarkatun man fetur na kasa a Najeriya wato NNPC a garin Eleme.

Hare-haren tsageru a yankin Niger Delta na Najeriya

Hare-haren tsageru a yankin Niger Delta na Najeriya

Kungiyar ta Avengers dai, ta ce za ta rufe dukkan shafukanta na sada zumunta a da ke kafar sadarwa ta Internet. A ranar Laraba ne dai kungiyar a adireshinta na Internet din, ta bayyana cewa wasu miyagu sun yi wa shafukanta na sada zumunta kutse inda suka ce kungiyar ce ta kai hari, dan haka nan gaba duk wasu bayanai da suka shafi kungiyar za su watsa shi ne ta adireshinsu na Intanet, maimakon shafukan sada zumuntar mallakar ta, inda ta kara da cewa ta ce duk wata kungiya da ke son ta yi wani abu na fito na fito da gwamnati ta yi a kasahin kanta ba tare da rabawa da kungiyarsu ba. Hare-haren kungiyar ta Avengers dai na yin nakasu ga harkokin hakar albarkatun man fetir da Najeriyar ke dagoro da shi a yankin na Niger Delta.