Ci gaba da garkuwa da wasu Jamusawa biyar a Yemen | Labarai | DW | 29.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da garkuwa da wasu Jamusawa biyar a Yemen

Mahukuntan kasar Yemen sun ce nan bada dadewa ba Jamusawan nan guda biyar da akayi garkuwa dasu za´a sako su.

Da alama dai wannan bayani na gwamnatin Yemen din ya biyo bayan irin kokarin da suke ci gaba dayi ne na ganin an sako wadan nan mutane biyar da a yau suka shiga kwana na hannu a hannun wadanda suka yi garkuwa dasun.

A dai jiya ne ofishin Jakadancin Jamus dake kasar ta Yemen ya bayar da sanarwar bacewar Jamusawan guda biyar, ciki har da tsohon Jakadan kasar a Amurka, wato Juergen Chroborg.

Rahotanni daga kasar ta Yemen sun nunar da cewa mambobin wata kabila ne ta Abdulla tayi garkuwa da Jamusawan guda biyar tare da direban su a gabashin kasar ta Yemen.

Bugu da kari Rahotannin sun kuma tabbatar da cewa mutanen da suka aikata wannan danyan aikin na son tursasawa gwamnatin ta Yemen ne sako yan kabilar su dake tsare a kasar , kafin sako Jamusawan a matsayin ban gishiri in baka manda