China za ta sassauta wa ′yan kasuwanta | Labarai | DW | 05.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

China za ta sassauta wa 'yan kasuwanta

Gwamnatin ƙasar China za ta jawo kamfanonin masu zaman kansu a harkar tattalin arzikinta, inda za a sayar musu wasu kamfanonin gwamnatin don bukasa tattalin arzikin ƙasa.

China Wirtschaft Premierminister Li Keqiang

Li Keqiang

Firimiyan ƙasar ta China ko kuma Sin wato Li Keqiang, shi ne ya bayyana haka a jawabin shekara shekara da ya yi gaban zauren majalisar al'ummar ƙasar ta China. Ƙasar a sanarwa kan sabbin tsare-tsaren tattalin arziki, cewa ta yi za ta bi hakan ne domin ci gaba da samun haɓakar arziki. Li ya ce bisa sabon tsarin gwamnati za ta sayar wa 'yan kasuwa kamfanonin da ta mallaka, kamar harkar jiragen ruwa da ɓangaren makamashi da kuma mai, kana da kamfanonin fasahar zamani, wadanda da ba safai ake samun kamfanoni masu zaman kansu na saya ba. Ƙasar ta China ta kuma sanar da tsarin ba da basuka domin tallafa wa 'yan kasuwa da suke samun haɓaka.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammad Nasiru Awal