1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China: karshen dokar killacewa

Abdourahamane Hassane
December 26, 2022

Kasar China za ta kawo karshen dokar killacewa ga wadanda suka shiga kasar baki daga ranar takwas ga watan Janairu na sabuwar shekara ta 2023.

https://p.dw.com/p/4LRJj
Bildergalerie | China |  Omicron erreicht Chinas Festland
Hoto: NOEL CELIS/AFP

Hukumomin kiwon lafiya na kasar sun ce daga ranar takwas ga watan Janairu za a fara aiwatar da dokar bayan da aka dage yawancin matakan yaki da COVID-19 da ke aiki ,a farkon watan Disamba. Daga wata mai zuwa gwajin daya ne kawai na kasa da sa'o'i 48 za a bukata daga matafiyi kafin shiga China. Kasar China ita ce kasa daya tilo mai karfin tattalin arziki da ta ci gaba da sanya dokar hana zirga-zirga da kuma killace baki 'yan yawan shakatawa da ke shiga kasar saboda karuwar cutar corona da ake samu a kasar a baya-baya nan.